Sai Atiku! Matashi ya fara tattaki daga Zaria zuwa Abuja domin nuna goyon bayan sa ga dan takarar PDP

Atiku’s choice, a return to corruption era – Lai Mohammed

Yace farin cikin nasarar da Atiku yayi na zama dan takarar PDP ne ta ingiza shi wajen yin  wannan tafiya kuma Atiku kadai zai iya warware matsalar da 'yan Najeriya ke fama da ita.

Kamaludden Bashir shine matashin da ya fara tattaki da kafa daga garin Zaria na jihar Kaduna zuwa birnin tarayya na Abuja don ya nuna goyon bayan sa ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Matashin wanda ya fara tafiyar tashi daga unguwar Kwarbai ya bayyana ma manema labarai cewa saida ya nemi amincewar iyayen sa inda suka yi  mai addu’ar fatan Alheri sannan ya kama hanya.

A labarin da jaridar Daily post ta fitar, Matashin ya fara tafiyar tasa tun daga ranar litinin 8 ga watan Oktoba kuma ya isa garin Kaduna washe garin ranar Talata 9 ga wata.

Yace farin cikin nasarar da Atiku yayi na zama dan takarar PDP ne ta ingiza shi wajen yin  wannan tafiya kuma Atiku kadai zai iya warware matsalar da ‘yan Najeriya ke fama da ita.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu an mai fashin kudi da kuma abincin da yayi guzuri dashi amma wannan bazai hanashi ci gaba da tafiya ba, kuma yana tsammanin zai kwashe kwanaki 5 yana wannan tafiya kafin ya isa Abuja.

Ya bayyan cewa zai yi kokarin ganin ya ja ra’ayin matasa ‘yan uwanshi akan hanya dan su yi wannan tafiya tare.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*