Biki bidiri: Ado Gwanja ya saki kyawawan hotunan kafin aure na shi da amaryar sa mai jiran gado

Ya saki hotunan a shafin sa na Instagram tare da rubuta wasu kalaman soyayya na nuna farin cikin sa.

Shahararren jarumin Kannywood kuma fitaccen mawaki, Ado Isah Gwanja, ya fitar da wasu kayatattun hotunan kafin aure na shi da amaryar sa mai jiran gado.

Ya wallafa hotunan da suka birge a shafin sa na Instagram tare da bayyana farin cikin sa bisa damar da ya samu na samun sahibar shi.

 

Hotunan dai sun fito bayan kwanaki da sanar da ranar da za’a daura auren su.

Mawakin wanda ake wa lakabi da “Limamin mata” zai angwance ga masoyiyarashi, Maimuna Kabir Hassan cikin wanan wata.

Za’a daura auren su ranar 12 ga watan Oktoba a jihar Kano dai dai karfe hudu na yamma.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*